Kasar Ingila ta tilastawa baki killace kansu a otel saboda Korona

Dukkannin bakin da suka taho daga kasashen turai da suka hada da mazauna Burtaniya wadanda suka sauka a kasar Ingila a tialsta musu kebe kansu a otel otel.

Kasashe 33 da dokar ta shafa sun hada da kasar Portugal, Brazil da kuma Afrika ta kudu.

Sabuwar dokar wadda akayi ta da nufin hana shigowa da cutar corona daga wasu kasashen, ta shafi dukkannin matafiyan da suka kasance a kasashen da dokar ta shafa na tsawon kwanaki 10. Wadanda za’a killace sun dole ne suyi gwaje gwajen da ya kamata, sannan su biya kudi yuro 1,750 sannan su killace kansu na tsawon kwanaki 10 a otel otel din kasar.

Comments (0)
Add Comment