Jakadan kasar China a Najeriya,Cui Jianchun ya shawarci gwamnatin tarayyya ta kara kudaden da ta ke kashewa a fannin ilimi, samar da abinci, gidaje da kiwon lafiya domin yaki da talauci.
Mista Jianchun ya bada wannan shawara ne jiya Abuja yayin kaddamar da littafin da shugaban kasar Chana Xi Jinping ya rubutu, mai sunan mu tashi mu yaki talauci, wanda aka fassara shi zuwa yaran Hausa.
Yace littafin an rubuta shine tun a shekarar 1988, wanda ke dauke da wasu ra’ayoyi na shugaban kasar Chana dangane da hanyoyin da za’a bi a yaki talauci.
Tunda farko,sakataran gwamnatin tarayya George Akume, yace littafin da aka kaddamar na dauke da hanyoyin da yan Najeriya zasu fita daga kangin talauci.
A cewar sa, sama da yan Najeriya milyan 80 na rayuwa cikin talauci musamman a yankin Arewa.