Kanada ta zama ƙasa ta baya-bayan nan ta yammacin duniya, da ta sanya sunan rundunar sojin Iran cikin jerin ƙungiyoyin ƴan ta’adda.
Dama ƴan siyasa a ƙasar ta nahiyar Amurka ta Arewa, sun jima suna fafutukar ganin an aiwatar da hakan.
Wannan na nufin za a hana dubban manyan jami’an rundunar juyin-juya halin da ake kira IRGC shiga ƙasar ta Kanada.
Ministan tsaron ƙasar Dominic LeBlanc, ya ce Tehran, ta jima tana nuna halin ko-in-kula ga ƴancin ɗan’Adam amma lokaci ya yi da za a taka mata birki.
A lokacin gwamnatin Donald Trump, Amurka ta sanya rundunar sojin ta juyin-juya-halin Iran cikin jerin ƙungiyoyin ta’adda na duniya.
Wannan shi ne karon farko da Amurka ta ayyana rundunar sojin wata ƙasa a matsayin ƙungiyar ta’adda
Iran ta mayar da martani a lokacin inda ita ma ta ayyana dakarun Amurka da ke yankin Gabas ta Tsakiya a matsayin ƙungiyar ta’addanci