Cibiyar Kula da Yaran Da Aka Ciwa Zarafi wanda take Asibitin Gambo Sawaba ta Jihar Kaduna, ta ce ta samu rahoton korafe-korafen Cin Zarafin Yara yan Kasa da shekara 17 kimanin su 652 tsakanin watan Fabreru na 2019 zuwa Agusta na 2021.
Shugabar Cibiyar Hajiya Amina Ladan, ita ce ta bayyana hakan a lokacin da take zantawa da Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa NAN a Zaria.
A cewarta, a ranar 7 ga watan Fabreru na shekarar 2019 ne aka kafa Cibiyar, inda kuma cikin shekarar suka samu rahoton fyade 135.
A shekarar 2020 kuma suka samu rahoton fyade 346, inda ta kara da cewa a shekarar da muke ciki kuma kimanin korafe-korafen fyade 171 cibiyar ta samu.
Shugabar Cibiyar ta ce mafiya yawan korafe-korafen fyaden ya kunshi wanda aka yiwa Maza da Mata yan kasa da shekara 17, wanda kuma Jami’an tsaro ko shugabannin gargajiya ne suka kaiwa rahoton.
Haka kuma ta ce Cibiyar ta samu karanci rahoton Mazan dake cin zarafin Maza saboda tabuwar hankali.
Kazalika, ta ce an gurfanar da masu aikata laifin a gaban Kotu.