Wani babban jami’in kamfanin man fetur na Dangote ya yi zargin cewa waɗansu manyan kamfanonin man fetur na ƙasashen waje na haifar da tarnaƙi wajen hana shi samun ɗanyen mai a cikin Najeriya.
A cewarsa, hakan ya tilasta wa kamfanin Dangote dogaro da ɗanyen man fetur mai tsada daga ƙasashen waje.
Kamfanin man fetur na Dangote da aka kashe dala biliyan 20 ya soma aiki ne tun a cikin watan Junairu amma ya kasa cimma burinsa na tace mai ganga dubu 650 a kullum.
Dangote na shigo da ɗanyen mai jirgin ruwa (kago) 10 a duk wata kamar yadda waɗansu takardun ciniki suka nuna.
Ko dai manyan kamfanonin suna neman a biya su farashin da suka wuce kima ko kuma su ce ba su da man, in ji Devakumar Edwin, babban jami’in kamfanin man fetur na Dangote.
Ya ƙara da cewa kamfaninsu ya biya dala shida fiye da farashin da ake sayar da mai a kasuwar mai na duniya kuma a yanzu suna dogara ne da ɗanyen man da suke sayowa daga Amurka.
Edwin ya ƙara da cewa Najeriya ta bar kamfanonin da ke shigo da man fetur daga kasashen wajen wanda bai da inganci, a don haka a yanzu Dangote ya mayar da hankali waje sayar da tattacen mai a kasashen waje.