Kakakin majalisar wakilai, Tajudeen Abbas ya samar da kwamitoci na musamman guda 7

Kakakin majalisar wakilai Tajudeen Abbas ya samar da kwamitoci na musamman 7 domin taimakawa wajen tafiyar da harkokin majalisar.

Kakakin majalisar ya sanar da kafa wadannan kwamitoci yau a Abuja.

Kwamitocin sun hada da kwamitin tsaron cikin gida wanda Muhammad Danjuma zai jagoranta, da kuma kwamitin zabe wanda shi kakakin majalisar zai jagoranta, sai kuma kwamitin kafafan sadarwa karkashin jagorancin Bukar Ibrahim na jihar Yobe.

Sauran sun hada da kwamitin tsare-tsaren majalisa wanda Farfesa Juluis Ihonbvare  dan jam’iyyar APC daga jihar Edo zai jagoranta, sai kuma kwamitin dokokin kasuwanci karkashin Igariwey Iduma, daga jihar Ebonyi. Sai kuma kwamitin walwala,wanda Wale Raji daga jihar Legas zai kula da shi, da kuma kwamitin da’a da bada dama karkashin jagorancin Tunji Olawuyi na jihar Kwara.

Comments (0)
Add Comment