Kada Wani Ya Sake Kira Da Matar Shugaban ƙasa, Ku Kira Da First Lady -Aisha Buhari


Shekaru biyar bayan da Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ce babu wani abu mai kama da Ofishin Uwargidan Shugaban ƙasa a mulkinsa, sai ga shi a jiya Alhamis Aisha Buharin ta sanar da cewa daga yanzu ta ɗauki matakin cewa ana kiranta da sunan First Lady.


Aisha Buhari ta ce wannan mataki da ta dauka zai fara aiki ne nan take. A cewarta hakan zai taimaka wajen kawo karshen matsalar da matan gwamnonin Jihohi ke fuskanta wajen nasu muƙaman.


Idan dai za a iya tunawa a jawabin rantsuwar Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a mulkinsa na farko ya ambace ta da sunan Matar Shugaban ƙasa, Sannan kuma ba za a yi mata wani ofishi ba.


Aisha Buhari ta Shaida wannan sabon matakin da ta dauka ne yayin da take mika kyautuka ga matan gwamnonin da suka shude da na yanzu na jihohi 36 na fadin kasar nan.


Taron da aka gudanar da shi a babban ɗakin taro dake fadar Shugaban ƙasa dake Villa a Abuja.


Ta ce “Ni da kaina na zabi a kira na da matar shugaban ƙasa a lokacin da aka zabi Maigida na a karon farko. Amma sai dai daga baya na gano hakan ya haifar da rudani ga matan gwamnonin Jihohi kan walau a kira su da Uwargida ko Matar Gwamnonin jihohinsu.


“Don haka ku yafe min bisa wacan rudani da na haifar tun daga farko, amma daga yanzu na zabi a kirani da Uwargidan Shugaban ƙasa wato First Lady.” A cewa Aisha Buhari.

Aisha BuhariBuhariFirst Lady
Comments (0)
Add Comment