jirgin ruwa ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 80 a jamhuriyyar dimokradiyyar Congo

Kasar ta jamhuriyyar dimokradiyyar Congo ta saba fuskantar makamancin wannan hatsari, sakamakon matsalolin da suka dabaibaye bangaren sufurin jiragen ruwa.

Tuni shugaban kasar Felix Tshisekedi ya bada umarnin gudanar da bincike a kan lamarin don gujewa sake afkuwar irin wannan iftila’I a nan gaba.

Shugaban ya kuma mika ta’aziyarsa ga iyalan wadanda suka mutu a hatsarin tare da ba da umarni ga ma’aikatan lafiya kan su ci gaba da kula wa da wadanda suka jikata.

Hakazalika ana alakanta yawan faruwar hatsuran jiragen ruwan ne da daukar kaya da mutane fiye da kima, wanda hakan ya samo asali ne sakamakon karancin hanyoyin sufurin motoci da jamhuriyyar dimokradiyyar Congon ke fama da shi.

Comments (0)
Add Comment