Jirgi mai saukar Ungulu Helikwafta na farko da aka haɗa a ƙasar nan ya kusa kammaluwa, kuma shirye-shiryen gwajin tashinsa sun yi nisa.
Hukumar NASENI, mai kula da binciken inganta aikin injiniya da kimiyya da ƙere-ƙere ce ta bayyana haka.
Ta sanar da wannan nasara ce a yayin wani taron kwararru da ta gudanar a Kaduna ranar Laraba.
Manajan Ayyuka a Cibiyar Binciken Kera Jirage na NASENI da ke Kaduna, Injiniya Kareem Aduagba, ya bayyana cewa yanzu sun kai matakin ƙarshe kuma nan gaba kaɗan za su yi gwajin tashin jirgin farko ƙirar Najeriya.
Ya ƙara da cewa suna ƙera jiragen ne ta hanyar inganta ayyuakansu daga abin da aka saba.