Jihar Legas Ta Hana Duk Taron Da Ya Wuce Na Mutane 50 Har Masallatai Da Coci-Coci

Yan awanni kadan bayan sanarwar dakatar taron ibadar da ya kunshi mutanen da suka haura 50 a jihar Legas, Jihar, ta sanar da rufe makarantun gwamnati da masu zaman kansu.

Rufewar za ta fara aikine ranar Litinin 23 ga watan Maris na wannan shekarar.

Bayanin rufewar, ya fitone daga bakin Kwamishiniyar Ilimi ta jihar, Mrs Folashade Adefisayo.

Kwamishiniyar ta kara da cewa rufewar ta zama dole domin a kare malamai da dalibai daga barazanar annobar coronavirus.

A jihar Legasne aka fi samu wadanda suka kamu da cutar a nan Najeriya, inda a halin yanzu akwai mutane shida da ake kulawa da su jihar bayan an tabbatar da sun kamu da cutar.

Mrs. Folashade ta ce, yana da matukar muhimmanci iyaye su kula da yayansu ta hanyar gudar shiga taron jama’a da tare da amfani da hanyoyin tsaftace kai don gudun kamuwa da cutar.

Ta kuma ce ba’a rufe makarantun da nufin firgita jama’a ba, sai domin a rage barazanar yaduwar cutar da ta zama annoba a duniya.

COVID - 19KORONA
Comments (0)
Add Comment