Mai girma Gwamnan Jihar Jigawa ya umarchi maikatrar Lafiya karkashin kwaminshinan Lafiya Dr. Abba Zakari Umar dasu tantance yara 60 Yan asalin jihar Jigawa masu sha’awar karatun likita wato medicine domin gwamnati ta dauki nauyin su zuwa karatu kasar waje.
Za a dauki yara biyu daga kowacce mazabar dan majalissa.
Ana bukatar yara Yan kasa da 23, wadanda suke da a kalla credit 5 a Biology, Chemistry, Physics, English da mathematics.
- Majalisar Dokokin Legas ta sake zaɓen Obasa a matsayin kakakinta
- An yi garkuwa da wani ɗansanda a Abuja
- Gwamnatin Jihar Yobe ta bayar da tallafin karatu da ya kai Naira biliyan 2.22 ga dalibai 890
- Kungiyar NANS ta yi barazanar fara zanga-zanga a fadin Najeriya
- Kotun ta yi watsi da bukatar hana jami’an gwamnati tafiya kasashen waje don neman magani
Wannan shiri na yayan talakawa ne kawai wadanda suka gama karatun secondary a makarantun gwamnati kuma za a zakulo yaran bisa chancanta kawai.
Ana bukatar daukar a kalla mata 30, maza 30.
Duk me sha’awa yakai takardunsa ofishin kwamishinan lafiya na Jigawa Dr. Abba Zakari Umar daga ranar Juma’a 3rd July.
Kwamishinan lafiya na jihar Jigawa Dr. Abba Zakari Umar yace za’a rufe karbar takardun ranar 10 ga July a kuma yi jarrabawar tantancewa ranar litinin 13th July 2020.