Jigawa, Kano da Katsina zasu daina korafin wutar lantarki

Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki Shiyyar Kano (KEDCO) yace ya dauki matakan da suka kamata wajen kawo karshen korafe-korafen masu sabuwar mita da ake saka mata kati.

Jihoshin dake karkashin KEDCO sune Jigawa da Kano da Katsina.

Shugaban Sashen Yada Labarai na Kamfanin, Ibrahim Shawai, ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a Kano.

Ibrahim Shawai ya sanar da cewa kamfanin ya dauki matakan inganta ayyukansa domin magance yawan korafe-korafe akan sabuwar mitar.

Yayi nuni da cewa an samu jan kafa wajen fara aiwatar da sabon kudin wuta kasancewar masu sabuwar mitar sun ki amincewa da katin wutar da suka saya farawa daga ranar 1 ga watan Satumba.

Yace kamfanin ya bayar da muhimmanci wajen magance korafe-korafen da suka shafi mita, domin biyan bukatar abokan hulda.

Jigawa
Comments (0)
Add Comment