Jawabin Sarkin Kano Kan Matsalolin Arewa Da Suka Jawo Cece-Kuce

Mai Martaba Sarkin Kano, Mallam Muhammadu Sanusina II yace ‘yan Arewana daf da ruguza kawunansu matukar suka kasa magance dumbin matsalolin dake fuskantarsu.

Sarki Sanusi wanda yayi jawabi a bikin cikar Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, shekaru 60 a duniya, wanda aka gudanar ranar Litinin a Kaduna, ya lissafa manyan matsalolin dake fuskantar yankin da fatara da talauci, da miliyoyin yaran da basa zuwa makaranta da karancin abinci mai gina jiki da shaye-shayen miyagun kwayoyi da almajiranci da kuma rikicin Boko Haram.

https://www.sawabafm.com/wani-mutum-yayi-%c6%99arar-matarsa-saboda-tana-haifa-masa-%c6%b4a%c6%b4a-munana/

Sarkin wanda ya kafe kan cewa babu wani shugaba a Arewa na gaske da yake farin ciki da matsalolin, yace akwai bukatar Arewa ta daina dogaro da tsarin kaso da raba dai-dai a kasar nan.

Yace dole a magance matsalolin dake fuskar yankin cikin gaggawa.

Sarkin ya fadi hakanne mako guda bayan Bankin Duniya ya fitar da wani rahoton dake nuni da cewa, 87% cikin 100 na talakawan Najeriya suna zaune ne a yankin Arewa.

Kano
Comments (0)
Add Comment