Jam’iyyar PDP ta bukaci kotu da ta tumbuke gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe saboda karbar mukamin zartarwa a matsayin shugaban riko na jam’iyyar APC.
A karar da ta shigar a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja a jiya, PDP ta ce hada ofishin gwamnan da wani mukamin zartarwa ya saba wa kundin tsarin mulki.
Jam’iyyar PDP ta ce kujerun gwamnan jihar Yobe da na mataimakin gwamna, Idi Gubana, sun zama babu kowa akai bayan Mala Buni ya karbi mukamin APC.
Jam’iyyar adawar ta nemi a bawa dan takarar gwamnan ta a zaben shekarar 2019, Umar Damagum, da mataimakinsa, Baba Aji, da su maye gurbin Mala Buni da mataimakin sa.
Takardar kotun ta nuna jam’iyyar PDP, tare da Umar Damagum da Baba Aji, a matsayin wadanda suka shigar da karar a tare.