Jam’iyyar APC ta yi Sanata Mohammed Ali Ndume afuwa

Jam’iyyar APC ta ce ta yi wa dan majalisar dattawa kuma tsohon mai tsawatarwa na majalisar, Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu, Mohammed Ali Ndume afuwa, kan yadda ya fito fili ya soki salon jagorancin shugaban kasa Bola Tinubu da jam’iyya mai mulki kan kunci da tsadar rayuwa da ake fuskanta a fadin kasar. 

Sakamakon wannan sukar, aka tsige Ndume daga mukaminsa na babban mai tsawatarwa a majalisar dattawa saboda jajircewarsa na fadin gaskiya ga masu mulki a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin kwanan nan.

Majalisar Dattawa a zamanta na ranar 17 ga watan Yuli ta sauke Ndume a matsayin mai tsawatarwa sannan ta maye gurbinsa da Sanata Mohammed Tahir Monguno. Da yake jawabi ga manema labarai bayan taron kwamitin gudanarwa na jam’iyyar APC (NWC) tare da Sanata Ndume a Abuja a jiya Talata, Ganduje ya ce, bangaren gudanarwar jam’iyyar zai rubutawa majalisar dattawa cewa, majalissar ta yi wa Ndume afuwa.

Comments (0)
Add Comment