Jam’iyyar (APC) da ‘yan takararta sun shigar da kara a kotun sauraron kararrakin zabe a jihohin Kano da Filato da Ribas suna kalubalantar sakamakon zaben gwamnan da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris.
Jam’iyyar APC reshen jihar Kano ta shigar da kara a gaban kotun sauraron kararrakin zabe ta Kano tana kalubalantar zaben Kabir Yusuf na jam’iyyar (NNPP) a matsayin zababben gwamna.
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaben da aka gudanar a ranar 18 ga Maris, 2023.
Gawuna ya amince da shan kaye kuma ya taya Yusuf murna mako guda da bayyana sakamakon karshe.
Sai dai jam’iyyar APC a cikin karar mai shafika biyar tana zargin cewa Abba Kabir Yusuf bai cancanci tsayawa takara ba, bisa zargin cewa sunansa ba ya cikin jerin ‘yan jam’iyyar NNPP da aka aika wa INEC. Sai dai kuma dan takarar gwamna na jam’iyyar APC, Nasiru Yusuf Gawuna, bai shiga jam’iyya ba a cikin karar saboda jam’iyyun da abin ya shafa sun hada da APC, mai shigar da kara da kuma NNPP, Abba Kabir Yusuf.