Jami’in kwastam ya mutu yana tsaka da amsa tambayoyi a majalisa

Wani jami’in hukumar kwastam ta Najeriya ya mutu yayin halartar zama don amsa tambayoyi a majalisar wakilai.

Wata sanarwa da shugaban kwamitin harkokin yada labarai na majalisar Akin Rotimi ya fitar a ranar Talata, ta ce jami’in ya “gamu da yanayi na rashin lafiya nan take” yayin amsa tambayoyi, al’amari da ya faru da misalin karfe 1 na rana.

Ya ce, “Mun kaɗu matuka da mutuwar jami’in na kwastam wanda ya halarci zauren majalisar.

Ya ce jami’an lafiya a asibitin majalisar wakilan sun yi kokari wajen bai wa jami’in kulawa, amma sai rai ya yi halinsa.

Sai dai majalisar ba ta bayyana asalin jami’in ba, domin martaba iyalansa.

Comments (0)
Add Comment