An bayyana Jami’ar gwamnatin tarayya dake Dutse babban birnin jihar Jigawa, a matsayin jami’ar da ta fi fice a cikin jami’oi 12 da gwamnatin tarayya ta gina a 2011.
Shugaban hukumar dake kula da jamioi ta kasa (NUC) Farfesa Abubakar Adamu Rasheed ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Abuja.
Ya ce jami’ar ta FUD ta kaddamar da bikin sababbin dalibai har sau 8 daga cikin wadanda aka kirkire su tare yayin da su kuma ke kokarin gudanarda bikin a karon farko.
Rasheed ya ce an samu cigaba sosai a jami’ar sakamakon fadi tashin da shugabannin jami’ar ke yi karkashin jagorancin Farfesa JD Amin, da kuma Farfesa Fatima Batul-Muktar.
Kazalika ya yabawa al’ummar jihar Jigawa da kuma gwamnatin jihar bisa taimakon jami’ar wajen gudanar da ayyukanta.