Jami’an Operation Whirl Punch sun lalata wani sansanin ‘yan ta’adda a jihar Kaduna

Rundunar sojin saman Najeriya, NAF, ta ce rukuninta na Operation Whirl Punch, OPWP, ta lalata wani sansanin ‘yan ta’adda da ke dajin Yadi da ke karamar hukumar Giwa a jihar Kaduna.

Mataimakin daraktan hulda da jama’a da yada labarai na NAF, Kaftin Kabiru Ali ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin a Abuja.

Ali ya ce an aiwatar da aikin ne biyo bayan sahihan bayanan sirri da ke nuna dimbin ‘yan ta’adda da ma’ajiyar makamansu a dajin Yadi.

Ali ya ci gaba da cewa, bayanan sirri da hukumar NAF ta samu sun nuna cewa sansanin kayan aikin mallakar fitaccen sarkin yan’ta’adda ne Kadage Gurgu  wanda ya kasance yana bayar da matsuguni ga jiga-jigan ‘yan ta’adda da suka yi kaurin suna a jihohin Sokoto da Zamfara.

“Rahotanni daga majiyoyi masu zaman kansu, ciki har da masu ba da labari na cikin gida da ke kewayen yankin,  sun tabbatar da cewa an lalata sansanin kayan aikin kwata-kwata kuma an kashe ‘yan ta’adda da dama a sakamakon harin.

Ya kara da cewa”Rundunar NAF, tare da hadin gwiwar sojojin saman, za su ci gaba da mamaye fagen fama ta hanyar wayar da kan jama’a game da halin da ake ciki, da ci gaba da sintiri, da kuma dakile hare-haren ‘yan bindiga a yankin da ke da alhakinta da kuma makwabtan jihohin ” kuma “Wannan yana da nufin kawar da ayyukan ta’addanci da aikata laifuka a yankin Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya.

Comments (0)
Add Comment