Isra’ila ta rusa sama da masallatai 1,000 a Gaza

Kusan Masallatai 1,000 Israila ta rugurguza a hare-haren da ta kai wa Gaza a shekarar da ta wuce, in ji hukumomin Falasdinawa.

A wata sanarwa da Maaikatar Harkokin Addinin Falasdinu ta fitar, ta ce masallatai 815 ne Israila ta rugurguza, inda kuma ta latata 151.

Ma’aikatar kuma ta ce makabartu 19 da coci uku Israila ta lalata wa Falasdinawa a shekarar 2024. Sun kuma kai hare-hare 20 a Gabar Yamma da Kogin Jordan da lsraila ta mamaye, sannan Yahudawa ‘yan kama-wuri-zauna sun kutsa kai cikin Masallacin Kudus sau 256 a shekarar da ta wuce.

Comments (0)
Add Comment