Asusun kiwon lafiya na jihar Jigawa yace kawo yanzu asibitoci masu zaman kansu guda 10 ne suka nuna sha’awarsu ta shiga shirin asusun adashen gata na kiwon lafiya na jiha.
Sakataren zartarwa na asusun Dr Nura Ibrahim ya sanar da haka ga Radio Jigawa.
Yace daga cikin asibitocin masu zaman kansu da suka yi rijistar shiga shirin sun hadar da guda uku a garin Hadejia da daya a Dutse da daya a Ringim da uku a Kazaure da kuma daya a Maigatari da daya a Babura.
- Hukumar Hisbah ta fara kama wanzamai da matasan da ke askin zamani
- Mataimakin gwamnan Kano ya jagoranci tawaga zuwa Edo kan kisan matafiya a Uromi
- Matatar Dangote ta rage farashin man fetur zuwa Naira 865
- Gwamnoni 11 na jam’iyyar PDP sun shigar da Tinubu kara a gaban Kotun Koli
- Gwamnan Jihar Filato yayi Allah wadai da kisan mutane 50 da aka yi a jihar
Dr. Nura Ibrahim yace kawo yanzu sun shigar da ma’aikatan jiha da kananan hukumomi da na sashen ilmi dubu 25 da 116 ne aka yiwa rijista kawo yanzu.
Yace a mako mai zuwa jirgin rijistar zai ziyarci kananan hukumomin Mallam Madori da Auyo da Kaugama.