Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta kare karin kasafin kudi na Naira biliyan 18 a majalisar dokokin tarayya, da nufin magance matsalar walwala da jin dadin ma’aikata da kudaden alawus-alawus.
Shugaban hukumar, Mahmood Yakubu ne ya jagoranci tawagar hukumar kare karin kasafin kudin a gaban kwamitin majalisar wakilai kan harkokin zabe da kuma kwamitin majalisar dattawa kan INEC a ranar Laraba.
Idan ba a manta ba a baya hukumar ta aike da kudirin naira biliyan 18 ga majalisar zartarwa ta tarayya, ta kuma kare kudurin a gaban majalisar zartarwa, inda ta mika ta ga majalisar dokoki domin amincewa.
Farfasa Yakubu a lokacin da yake kare kasafin kudin, ya bayyana cewa Naira biliyan 10.6 daga cikin kudaden za su baiwa hukumar damar biyan ma’aikatanta karin kashi 40 na alawus alawus da gwamnatin tarayya ta amince da su a watan Afrilun 2023. Ya ce hukumar za ta kashe naira biliyan 1.6 wajen gudanar da zabukan cike gurbi guda 11 da suka hada da mazabu biyar na tarayya da na jihohi hudu da kuma na ‘yan majalisar dattawa biyu.