INEC na shirin tura ma’aikata 46,084 domin gudanar da zaben gwamna a jihohin Bayelsa, Imo da Kogi

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta ce ta na shirin tura ma’aikata dubu 46,084 domin gudanar da zaben gwamna na ranar 11 ga watan Nuwamba a jihohin Bayelsa, Imo da Kogi.

Shugaban hukumar Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana haka a taron da hukumar ta saba yi duk rukuni uku na shekara da kwamishinonin zabe a Abuja.

Mahmud Yakubu ya kuma ce wakilan jam’iyyar dubu 137 da 934 da ke wakiltar jam’iyyun siyasa 18 da suka kunshi kuri’u 130,093 da kuma wakilai 7,841 za su kasance a filin zaben.

Mahmud Yakubu ya ce irin wannan gagarumin aikin na bukatar samar da ingantaccen muhalli wanda a cewarsa ya wuce hurumin hukumar nan take.

Da yake nanata damuwar hukumar game da matsalar rashin tsaro da tashe-tashen hankula masu nasaba da zabe a jihohin uku, Farfasa Yakubu ya ce hukumar ta INEC ta tabbatar da cewa an samar da isassun jami’an tsaro.

Comments (0)
Add Comment