Ina alfahari da samun dimbin goyon bayan da ake bukata domin zama ‘yartakara – Kamala Harris

Mataimakiyar shugabar kasar Amurka Kamala Harris ta ce tana alfahari da samun dimbin goyon bayan da ake bukata domin zama ‘yartakarar jam’iyyar Democrat a zaben shugaban kasa.

Tana magana ne bayan binciken da aka gudanar ya gano cewa za ta samu yawan wakilan masu zaben da ake bukata wajen zabarta a matsayin ƴartakarar jam’iyyar Democrats, bayan da shugaba Joe Biden ya janye daga takara.

Zuwa yanzu, dukkan wadanda ake tunanin za su yi takara da ita sun mara mata baya, Tun da farko ta fara yakin neman zabenta a Delaware mahaifar shugaba Biden, inda ta shaidawa magoya bayanta cewa za ta tsallakar da Amurkawa tudun mun tsira daga abin da ta kira barazanar Donal Trump

Ta yi alkawarin inganta rayuwar marasa karfi, da yaki da mallakar bindiga da kuma kare ‘yancin mata na zubar da ciki idan aka zabe ta.

Comments (0)
Add Comment