IBB bai taɓa gallazawa Tinubu ba a zamanin mulkin soja ba

Fadar shugaban kasa tace ko kadan tsohon shugaban kasa na mulkin soja janar Ibrahim Badamasi Babangida bai taɓa gallazawa Tinubu ba a zamanin mulkin soja ba, kamar yadda tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo, ya faɗa. 

A makon da ya gabata, Osinbajo ya yi wannan magana yayin da yake gabatar da jawabi a matsayinsa na mai nazartar littafin tarihin Babangida, mai suna *A Journey in Service*, a taron ƙaddamar da shi da akayi a Abuja. 

Inda yace ya tuna yadda Tinubu, a matsayinsa na Sanata, ya bijire wa rusa Majalisar Dattawa bayan soke zaɓen Shugaban Kasa na ranar 12 ga Yuni, 1993. 

Sai dai Onanuga ya musanta wannan batu, yana mai cewa Babangida, a maimakon haka, ya taimaka wajen shigar Tinubu siyasa, tare da ƙarfafa kwarin gwiwar sabbin ‘yan siyasa daga bangaren kwararru da masu zaman kansu a farkon shekarun 1990. 

Comments (0)
Add Comment