Hukumomin Uganda na tsare da tsohon mataimakin ministan harkokin tsaron cikin gidan Kenya Stephen Tarus bisa zargin safarar zinare zuwa cikin ƙasar ta hanyar amfani da takardun jabu.
Wata kotun yaƙi da cin hanci da rashawa ta Uganda ce ta kama.
Hukumar tara kudaden shiga ta Uganda (URA) ta ce an kama Mista Tarus ne a makon da ya gabata, kuma an gurfanar da shi a gaban wata kotun yaki da cin hanci da rashawa ta ƙasar ranar Larabar da ta gabata, bisa samunsa da laifin karkatar da takardun fitar da kayayyaki zuwa ƙasashen waje.
Hukumar tace takardun cinikin ba bisa ka’ida ba sun haifar da asarar kuɗaɗe ga gwamnatin Uganda.
An tuhume shi da yin jabun takardu na fitar da kaya akan kilogiram 13 na zinari da darajarsu ta kai $30,000.
Dan shekara 57 ya taɓa rike mukamin mataimakin minista a karkashin marigayi shugaba Mwai Kibaki da kuma jakadan Kenya a Australia tsakanin shekarar 2009 zuwa 2012. Ya kuma zama ɗan majalisa tsakanin 2003 zuwa 2007.