Hukumar Zaɓe ta Jihar Filato PLASIEC ta sanar sakamakon zaɓen ƙananan hukumomin jihar, da ta gudanar a ranar Larabar nan da ta gabata.
Sakamakon zaɓen, ya nuna cewa Jam’iyyar PDP ta lashe ƙananan hukumomi 15 daga cikin 17 da ke jihar.
Da yake bayyana sakamakon zaɓen, a jiya Alhamis a hedikwatar hukumar da ke Jos, shugaban hukumar zaɓen Mista Plangji Daniel ya bayyana cewa ƙananan hukumomin da jam’iyyar ta PDP ta lashe su ne Mikang, Shendam, Bassa, Riyom, Jos ta Kudu, Jos ta Gabas, Kanam, Qua’an Pan da Langtang ta Kudu.
Sauran sune Barkin Ladi da Jos ta Arewa, Kanke da Bokkos, Wase da kuma Mangu.
Shugaban hukumar zaɓen, ya yi bayanin cewa sauran ƙananan hukumomi guda biyun da ake jiran isowar sakamakon zaɓen su, sune Pankshin da Langtang ta Arewa.