Hukumar WHO za ta samar da magunguna kyauta ga yara masu fama da cutar sankara

Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta sanar da kaddamar da wani sabon shiri da zai samar da magunguna kyauta ga dubban yara masu fama da cutar sankara a kasashe masu matsakaicin karfi da marasa karfi.

A cewar hukumar, kasashen Mongoliya da Uzbekistan sun fara karɓar magungunan, tare da shirin isar da su zuwa Ekwado, Urdun, Nepal da Zambiya a matakin gwaji.

Wannan shiri zai amfani akalla yara 5,000 a bana, tare da fatan kaiwa kasashe 50 cikin shekaru biyar zuwa bakwai.

WHO ta ce mafi yawan yara a kasashe masu karancin tattalin arziki na rasa ransu sakamakon rashin magani mai inganci da katsewar jinya.

Comments (0)
Add Comment