Hukumar Raya Kogunan Hadejia-Jama’are ta bada tallafin irin shuka na Masara da Wake ga Hukumar bada agajin gaggawa ta Jihar Jigawa domin rabawa wadanda iftila’in ambaliyar ruwa ta shafa a wasu sassan jihar.
Da yake mika tallafin irin shukar ga sakataren zartarwar hukumar bada agajin gaggawa ta jiha, Alhaji Yusif Sani Babura, manajan daraktan hukumar raya kogunan Hadejia-Jama’are Alhaji Mahmud Da’u Aliyu ya ce sun bada tallafin irin ne domin tallafawa manoman jihar Jigawa da suka gamu da ta’addin ambaliyar ruwa.
Manajan daraktan wanda ya samu wakilcin mataimakin daraktan hulda da jama’a da harkokin baki na hukumar, Salisu Baba Hamza, ya ce irin yana yi da wuri kafin ruwa yayi yawa, inda ya bukaci manoma da su tabbatar sun yi amfani da irin domin inganta harkokin noman su.
Da yake karbar tallafin, sakataren zartarwar hukumar, Alhaji Yusif Sani Babura ya godewa hukumar bisa bada tallafin irin shukar, tare da bukatar karin tallafin makamancin wannan domin tallafawa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a jihar.
Irin shukar ya kunshi kilogiram dubu 1 da 360 na irin masara da kuma kilogiram dubu 1 da 360 na irin wake.