Hakumar wayar da kai ta kasa NOA reshen jihar jigawa ta soma shirya gangamin wayar da kan jama’a illolin ambaliyar ruwa.
Daraktan hakumar na jiha Ahmad Tijjani wanda ya jagoranci tawagar hakumar ta musamman zuwa Fadar hakimin Bulangu a karamar hakumar a jiya Litinin.
Tijjani yayi bayanin cewa an samar da shirin bisa manufar wayar da kan jama’a illoli da hatsarin date tattare da ambaliyar ruwa.
Ya jaddada cewa ibtila’ai na baya-bayan nan da ambaliyar ruwan ta haddasa ne ya tilasta musu shirya tarukan ga al’ummomin yankuna a fadin jiha.
Hakimin Bulangu Ibrahim Sulaiman ya yabawa hakumar bisa bullo da wannan shiri a kokarin wayar da kan jama’a muhimmancin kasancewa cikin koshin lafiya.