Hukumar NDLEA ta ayyana mutane huɗu da ake zargi da hannu a safarar miyagun ƙwayoyi tare da mashahurin dillalin ƙwaya, Alhaji Suleiman Aremu Ganiu, wanda aka fi sani da Barryshine, a matsayin waɗanda ake nema.
Waɗanda aka ayyana sun haɗa da Olarenwaju Ramon Abdulai, Oluwafemi Akande Abidoye, Olumuyiwa Olufemi Ilori da Alate Kafy Bakare Bukki.
Kotun Tarayya ta Lagos ta bada umarnin fitar da sunayensu da hotunansu domin a kama su, yayin da Barryshine ke fuskantar tuhuma a gaban kotu.
NDLEA ta bukaci duk wanda ke da bayani game da su ya tuntuɓi ofishinta mafi kusa ko ya kira lambar wayarta ta gaggawa.