Hukumar yaƙi da cutuka masu yaɗuwa a Najeriya ta NCDC ta tabbatar samun ƙarin mutum 418 da suka kamu da korona ranar Lahadi a ƙasar.
Cikin rahoton da ta wallafa, NCDC ta ce mutanen sun fito ne daga jiha 12. Jihohin su ne:
- Lagos-314
- Ogun-27
- Plateau-18
- Edo-17
- Enugu-11
- Abia-8
- Delta-7
- Bayelsa-5
- Kano-4
- Rivers-4
- Osun-2
- Oyo-1
Ya zuwa yanzu, jumillar mutum 217,481 ne suka harbu da cutar tun bayan ɓullarta. Haka nan ta kashe 2,981, sai kuma mutum 207,746 da aka sallama bayan sun warke.