Hukumar Kididdiga ta Kasa, NBS, ta ce hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ya ragu zuwa kaso 21.34 a ma’aunin shekara-shekara a watan Disamban 2022.
Hakan yazo ne cikin rahoton kididdigar farashin masu sayen kayayyaki da kuma hauhawar farashin kayayyaki na watan Disambar 2022 da aka fitar jiya a Abuja.
Rahoton ya ce adadin ya nuna raguwar kaso 0.13 idan aka kwatanta da na watan Nuwamban 2022 wanda yake da kaso 21.47.
Rahoton ya ce a ma’unin shekara-shekara, hauhawar farashin kayayyaki ya karu da kasho 5.72 idan aka kwatanta da adadin da aka samu a watan Disambar 2021, wanda ya kai kaso 15.63.
Rahoton ya ce hauhawar farashin kayan abinci a watan Disambar 2022 ya kai kaso 23.75 a ma’aunin shekara-shekara; wanda ya karu da kaso 6.38 idan aka kwatanta da kaso 17.37 da aka samu a watan Disamba na 2021.
Rahoton ya nuna cewa hauhawar farashin kayan abinci ya samo asali ne sakamakon hauhawar farashin biredi da hatsi da man girki da dankalin turawa da dawa da rogo da doya da kifi da sauran kayan abinci.