Hukumar Kwastam ta kama shinkafar kasar waje guda 212 wanda kudinsu ya haura N126m

Hukumar Kwastam ta Najeriya reshen jihar Kebbi ta kama wasu kayayyaki da suka hada da buhunan shinkafar kasar waje mai nauyin kilo giram 50 guda 212 wanda kudinsu ya haura N126m.

Kayayyakin a cewar Kwanturolan Hukumar Kwastam, Iheanacho Ojike, sun hada da lita 10,025 na man fetur da darajarsu ta haura N2m.

Ya ce fasa-kwauri na da illa ga tattalin arziki da kuma rayuwar ‘yan kasa, inda ya ce matakan da aka dauka don magance matsalar ne suka kai ga kwace kayayyakin.

Ojike ya ce za a mika kayan da aka kama masu alaka da kwayoyi ga hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa. Da yake magana kan samar da kudaden shiga a rundunar, kwanturolan ya ce ya komai tsaya cik a ‘yan kwanakin da suka gabata saboda rufe iyakokin da ke tsakanin Najeriya da Jamhuriyar Benin da Jamhuriyar Nijar.

Comments (0)
Add Comment