Hukumar Kwastam reshen Kano da Jigawa a jiya ta sanar da kwace haramtattun kayayyaki guda 398 da kudinsu ya kai biliyan 1 da miliyan 21 da Naira dubu 556 da 789 da kuma kobo 98.
Kwanturolan hukumar kwastam reshen Kano da Jigawa, Suleiman Pai Umar ya ce an kama haramtattun kayayyakin daga watan Janairu zuwa yau.
Da yake zantawa da manema labarai, ya bayyana cewa, sun kama wasu da dama da ake zargi da aikata laifin, wasu daga cikinsu an mika su ga hukumomin da abin ya shafa domin cigaba da bincike da gurfanar da su gaban kuliya, yayin da wasu kuma aka bayar da belinsu har zuwa lokacin da za a yanke hukunci a gaban kotu.
Ya bayyana cewa Kwanturola Janar na hukumar ya bayar da umarnin a dauki tsauraran matakai don kara karfafa kwazon jami’ansu kamar yadda wasu dokoki da ka’idoji suka tanada.
Daga cikin kayayyakin da rundunar ta kama kwanannan sun hada da shinkafa ‘yar kasar waje, taliya, kus-kus, madarar gari, madarar ruwa, kayan sawa gwanjo, sabulun Eva na kasashen waje, batiri, macaroni da fatun jakuna, da sauransu.