Hukumar Jin Dadin Alhazai Ta Jihar Edo Ta Bukaci Karin Masaukai 150

Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Edo ta bukaci karin matsuguni 150 daga hukumar alhazai ta kasa NAHCON domin daukar maniyyatan da suka biya.

Shugaban hukumar, Sheik Ibrahim Oyarekhua, wanda ya bayyana hakan, ya ce an baiwa alhazai har zuwa ranar 21 ga watan Afrilu domin kammala biyan kudin aikin hajjin.

Ibrahim ya ce an bai wa jihar gurbi guda 274, amma kimanin maniyyata 355 ne suka biya ko wani bangare na aikin hajjin Makkah, inda ya ce hasashensu ya kai 400.

Ya kara da cewa sun nemi karin gurbi guda 150, wanda ya gabatar da bukatar a hukumance ga shugaban NAHCON, kuma ya yi alkawarin tabbatar da bukatar.

Kudin Hajjin Alhazan Edo ya kai Naira 2,958,000 sannan ranar 21 ga watan Afrilu ne ranar da za a karkare biyan.

Ya kuma tuhumi maniyyatan da sukarasa biyan kudin kafin cikar wa’adin.

Comments (0)
Add Comment