Hukumar JAMB ta sanar da ranar fara jarrabawar wannan shekara ta 2025

Hukumar shirya jarabawar shiga jami’o’i ta Najeriya Jamb ta sanar da ranar 25 ga watan Afrilun da muke ciki a matsayin ranar fara jarrabawar wannan shekara ta 2025.

Cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Dakta Fabian Benjamin ya fitar, ya ce za a fara jarrabawar Jamb ta gwaji (Jamb-Mock) a ranar 10 ga watan na Afrilu.

Hukumar ta kuma buƙaci masu rubuta jarrabawar su fitar da katunan jarrabawar da ake kira ‘Exam Slip’ – waɗanda suka ƙunshi cikakkun bayanan ranar da mutum zai yi jarrabawar da lokaci da kuma wurin da zai yi ta.

”Ana buƙatar masu rubuta jarrabawar su fara fitar da katunan tun daga ranar 3 ga watan Afrilu, domin samun isasshen lokacin shirya wa jarrabawar”, in ji sanarwar.

Comments (0)
Add Comment