Hukumar Civil Defense a jihar Jigawa zata hada gwiwa da rundunar Operation Salama

Hukumar tsaro da kare rayukan al-umma ta  Civil Defense a jihar Jigawa, zata hada gwiwa da rundunar operation Salama, domin yin sintiri a karamar Hukumar Maigatari.

Kwamandan hukumar a jihar Jigawa , Muhammad Dawaki shine ya sanar da hakan a lokacin da ya ziyarci shugaban karamar hukumar Maigatari Uzairu Nadabo.

Yace hukumar zata aike da motar sintiri da jam’ai, da kuma kayayyakin aiki domin yin sintiri, tare da jami’an  tsaro na operation salama a yankin.

Muhammad Dawaki, ya kuma yaba da kyakkyawar dangantakar dake akwai a tsakanin jami’an hukumar, da sauran hukumomin tsaro dake aiki a yankin.

Kwamandan ya kuma sanar da bullo da wata sabuwar rundunar tsaro domin bada tsaro a makarantu.

A nasa jawabin shugaban karamar Hukumar Maigatari Mallam Uzairu Nadabo, ya yaba da wannan ziyara tare da godewa kwamandan bisa samar da karamin ofishin hukumar a garuruwan  Madana da kuma Galadi

Yace karamar Hukumar zata cigaba da tallafawa hukumar da sauran hukumomin tsaro dake aiki a yankin.

Comments (0)
Add Comment