Hukumar bunkasa ilmin manya ta jihar Jigawa ta kaddamar da rabon rediyo da kayayyakin koyan karatu da rubutu ta hanyar radio a unguwar Limawa dake karamar Hukumar Dutse.
Sakataren zartarwa na hukumar, Dr Abbas Abubakar Abbas wanda ya kaddamar da shirin yace hukumar bunkasa ilmin manya ta kasa ce ta bayar da rediyon da kuma sauran kayayyakin domin baiwa alummomin da aka yiwa rijistar shiga shirin ilmin manya ta hanyar rediyo.
Yace a garin Limawa mutane 50 da aka yiwa rijistar koyan karatu da rubutu ta hanyar rediyo ne za a baiwa kayayyaki domin bibiyar shirin da ake gabatarwa a gidan rediyon Jigawa a ranekun Asabar da Talata na kowane mako.
Dr Abbas ya kara da cewar mutane 300 ne zasu sami rediyon da sauran kayayyakin aikin da aka zabo daga yankuna 6 da suka hadar da Limawa da Taura da Kangire da Yalo da Jabo da kuma Garin Gambo.