Rundunar Hisba ta jihar Jigawa ta kai samame wasu gidajen sayar da barasa uku a garin Kazaure.
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da rundunar ta bawa manema labarai
Sanarwar ta ce a lokacin samaman rundunar ta yi nasara kama kwalaben barasa dubu daya da dari da sabain da shida. Daga nan sanarwar ta bukaci alumma da su cigaba da taimakawa rundunar ta hanyar ba ta bayanan wuraren aikata badala a sassan jihar nan.