Hatsarin mota ya ritsa da ayarin motocin Mataimakin Gwamnan jihar Sakkwato

Hatsari motar ya ritsa da ayarin motocin Mataimakin Gwamnan na jihar Sakkwato, Idris Gobir, inda hakan ya ’yi ajalin wani dan sanda da wani mai daukar hoto a tawagar.

Mutanen biyu sun gamu da ajalinsu a wannan hatsari ne bayan wata motar jami’an tsaro a cikin tawagar mataimakin gwamnan ta kwacce sannnan ta yi adungure a yankin  Yanrimawa da ke kan hanyar Goronyo-Sabon Birni

Hatsarin ya auke ne a lokacin da mataimakin gwamnan da ayarin nasa suke kan hanyarsu ta zuwa mahaifarsa, Sabon Birni a ranar Laraba.

An kama likitar bogi kan zargin kashe mai juna biyu a Kano

Darakktan yadaa labaran mataimakin gwamnan, a tabbatar da rasuwar dan sandan da ke tuka motar da kuma wani mai daukar hoto  da ke ciki motar.

A cewarsa an kai gawarwakin dakin ajiyar gawa. A lokacin da muka samu wannan labarin dai kakakin ’yan sandan Jihar Sakkwato, ASP Ahmed Rufa’i ya ce ba shi da labari wannan hatsari.

Comments (0)
Add Comment