Harshen larabci na daya daga cikin manyan yaruka mafiya farinjini da daukaka a duniya, kazalika shine yaren addinin musulunchi kuma yaren fiyayyen halitta, Annabi Muhammadu SAW.
Bisa la’akari da haka ne, majalisar dinkin duniya ta ware ranar 18 ga watan Disambar da muke ciki a matsayin ranar harshen ta duniya.