Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta jihar Kano karkashin jagorancin Muhuyi Magaji ta tabbatar da cewa lallai hukumar zata cigaba da bincikar Sarki Muhammadu Sunusi II kan zargin almubazzaranci da kudin Masarautar da ya kai har Naira N3.4bn.
Magaji ya bayyana haka ne a jiya Litinin yayin tattaunawa da manema labarai a Kano.
Ya shaida cewa a bisa sahalewa da halaccin sashi na 8 na kundin tsarin mulkin hukumar da yake shugabanta da aka yiwa kwaskwarima a shekara ta 2008, akwai tanadin dake nuna yadda hukumar ke da cikakken yancin gashin kanta ba tare da yi mata katsalandan daga kowa ba.
“A don haka hukumar bata karkashin wani ofishi ko wani mutum.”
“Saboda haka ne ita hukumar ta dukufa don yin duk mai yiwuwa kan ganin an tabbatar da bincike ta hanyar bin doka.”
Muhuyi ya kuma bayyana cewa hukumar ba ta fara binciken masarautar ba ne a lokacin da dangantaka tayi tsama tsakanin Gwamnatin Kano da Masarautar ba, face dai sun fara binciken ne a dalilin korafe-korafen da suka yi ta samu daga wurin wasu mutane masu kishin jihar.
Tun a wani lokaci a baya dai hukumar ta fara gudanar da bincike kan Sarkin na Kano amma daga bisa kurar ta lafa, sai dai a ‘yan baya-bayan nan bayan kammala zaben 2019 na Kano wanda hukumar zabe ta kasa INEC ta bayyana sunan Abdullahi Umar Ganduje a matsayin wanda ya lashe zaben, nan take sai liki ya tashi, aka sabunta bincike kan Sarkin da wasu ma’aikatan masarautar.
Haka zalika a wani yunkuri da ake ganin kamar na bita da kulli ne, Gwamna Ganduje ya kirkiro sabbin masarautu har 4 domin ragewa Masarautar Sarki Sunusi karfin iko, zargin da Gwamnatin Kanon ta sha musantawa.
Sabbin sarakunan da aka Kirkiro sune;
1. Sarkin Bichi Alhaji Aminu Ado Bayero.
2. Sarkin Rano Alhaji Tafida Abubakar Ila.
3. Sarkin Gaya Alhaji Ibrahim Abdulkadir Gaya.
4. Sarkin Karaye Alhaji Dr. Ibrahim Abubakar II.
A makon da ya gabata ne dai Hukumar ta yaki da cin hancin ta Kano ta shawarci Gwamnatin jihar da ta dakatar da Sarkin, bisa wannan shawara ce ta sanya Gwamnan rubuta wasikar neman ba’asi tare da bukatar Sarkin ya bayar da amsar Tuhumar da ake masa cikin yan awanni.
Amma a wani salo na in ka san wata baka san wata ba, Sarki Sunusi II ya amsa wasikar cikin Magana mai harshen damu da ta samu fassara daban-daban daga mutane da manazartan dake bin yadda alakar sabuwa da tsohuwar hukumar ke kasancewa.
Inda Sarkin ya masa wasikar da cewa; Sarki Sunusi ya gaji N1.8b ne bayan zama Sarki sabanin yadda ake zargi na N3.4b. Akan alkinta kudi kuwa, masarautar ta mayar da martanin cewa Sarki Sanusi II ba shi ne Akantan masarautar ba shi Sakatare, wanda hakan ke nufin Akanta ne kadai zai iya amsa tambayar kudi da yadda aka kashe su ba Sakatare ba.
Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewa a rahoton hukumar na farko da ta gabatarwa gwamnatin jihar ya nuna cewa hukumar ta gano anyi almubazzaranci da zunzurutun kudin masarautar karkashin shugabancin Sarki Sunusi daga shekarar 2014 zuwa 2017 da ya kai har Naira N3.4b.
Jama’a da dama a shafukan sada zumunta na cigaba da bayyana ra’ayoyi mabanbanta dangane da lamarin yayin da shi kuma Sarkin ke cigaba da daukar wankan kece raini har ma wasu na ganin don hasala wasu yake wankan.