Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya ce batun sauya jam’iyyar da ake yaɗawa ya yi ba gaskiya ba ne.
El-Rufai ya yi wannan jawabin ne biyo bayan raɗe-raɗin da ake yaɗawa cewa ya fice daga Jam’iyyar APC, ya koma Jam’iyyar PDP
A wani rubutu da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta, El-Rufai ya ce, “ku yi watsi da duk ƙarairayi da raɗe-raɗin da ake yaɗawa game da jam’iyyar siyasar da nake ciki. Tuni na umarci lauyoyina su yi abin da ya dace dangane da wasu yaɗa labaran na ƙarya.”