Har yanzu ba mu karɓi kuɗi daga ƙungiyar IPMAN ba domin sayen tataccen mai – Matatar Ɗangote

Matatar Ɗangote ta ce har yanzu ba ta karɓi kuɗi daga ƙungiyar dillalan mai ta kasa Ipman ba domin sayen tataccen mai.

Wata sanarwa da matatar ta fitar a shafinta na X, ta ce ana tattaunawa da Ipman, sai dai ta ce bai dace mambobin Ipman su nuna cewa suna fuskantar matsala ba wajen sayen tataccen mai daga matatar kasancewar “babu wata alaƙar kasuwanci ta kai tsaye da IPMAN.

A cewar matatar ta Ɗangote, cikin sanarwar da jami’inta na hulɗa da jama’a, Anthony Chiejina ya sanyawa hannu, “an biya kuɗin da ake magana a kai ta hannun kamfanin mai na NNPCL, ba wurinmu ba, inji shi. Matatar ta ce “suna son su jaddada cewa za su iya wadatar da Najeriya da duk albarkatun mai har da man jirgi, ta kara da cewa a yanzu, muna iya fitar da tirela 2,900 na mai, duk rana kuma muna fitar da albarkatun mai ta hanyar ruwa.” in ji matatar Ɗangote.

Comments (0)
Add Comment