Gwamnoni 11 na jam’iyyar adawa ta PDP sun shigar da kara a gaban Kotun Koli, suna kalubalantar ikon da Shugaba Bola Tinubu ke da shi wajen dakatar da tsarin gwamnati da aka zaba ta hanyar dimokuradiyya a wata jiha.
Karar da gwamnonin suka shigar na kuma kalubalantar ayyana dokar-ta-baci da aka yi a Jihar Rivers.
Jihohin da suka shigar da karar sun hada da, Adamawa, Enugu, Osun, Oyo, Bauchi, Akwa Ibom, Filato, Delta, Taraba, Zamfara da Bayelsa.
Idan dai za’a iya tinawa, a ranar 18 ga watan Maris, Shugaban kasa Bola Tinubu ya ayyana dokar-ta-baci a Jihar Rivers, tare da dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara, mataimakiyar gwamna Ngozi Odu, da dukkan ‘yan majalisar dokokin jihar na tsawon watanni shida.
Biyo bayan wannan mataki, Shugaba Tinubu ya nada tsohon hafsan rundunar sojin ruwa, Vice Admiral Ibok Ete Ibas (mai ritaya), a matsayin kwamishinan rikon kwarya domin jagorantar harkokin jihar har zuwa lokacin da dakatarwar za ta kare.
A gefe guda kuma, majalisar dokoki ta kasa ta goyi bayan matakin Shugaban kasa na dakatar da gwamnati a Jihar Rivers.