Gwamnatin tarayya zata samar da ayyukan yi Milyan 1

Mataimakin shugaban Kasa Kashim Shettima ya bayyana shirin gwamnatin tarayya na samar da ayyukan yi Milyan 1 a duniyar zamani ga Yan Najeriya.

Mataimakin shugaban kasar ya fadi haka ne a fadar shugaban kasa dake Abuja, yayin da ya karbi bakuncin tawaga daga Tarayyar kasar Koriya wanda  babban jami’in diplomasiyyar kasar Jang Sungmin ya jagoranta.

Ya tabbatar da irin kokarin da Najeriya ke yi wajen kala hulda tsakanin ta da Koriya, musamman a fannin kasuwanci,musayar fasaha da kuma kare zaman lafiyar duniya.

Mataimakin shugaban kasar cikin wata sanarwa da Daraktan yada labarai na ofishin sa ya fitar, ya tabbatar wa gwamnatin Koriyar  kudurin gwamnatin Tinubu na yin hadin gwiwa da Koriya domin karfafa dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu, musamman daidaita gibin cinikayya tsakanin su.

Ana sa jawabin babban jami’in Diplomasiyyar kasar Koriya Mista Jang Sungmin, ya taya Najeriya murnar rantsar da sabuwar gwamnati,inda ya mika goron gayyata ta musamman daga shugabar zuwa ga takwaransa na Najeriya, Bola Tinubu, domin halartar taron kasashen Afirka da Koriya ta Kudu da za a yi nan gaba kadan.

Comments (0)
Add Comment