Gwamnatin tarayya zata kaddamar da rabon tallafin kudade ga magidanta miliyan 15

Ministar harkokin jin kai da yaki da talauci Betta Edu tace gwamnatin tarayya zata kaddamar da tallafin tura kudade na wucin gadi ga magidanta miliyan 15 a ranar 17 ga watan da muke ciki.

Ta bayyana haka ne lokacin da ta bayyana a wani shirin tattaunawa na gidan television Channels Tv, watanni bayan gwamnatin tarayya ta dakatar da biyan tallafin man fetur.

A cewar ta, ma’aikatarta na aiki da masu ruwa da tsaki a dukkan fadin kasa domin yiwa wadanda suka cancanta rijistar tsarin domin cin gajiyar shirin. Yayin da take bayanin cewa wasu daga cikin mutanen dake cikin rijistar masu bukatar sun mutu, Betta tace za’a tabbatar da tantance wadanda ya kamata su ribaci shirin.

Comments (0)
Add Comment