Gwamnatin tarayya tabbatar da ɓullar cutar anthrax a kasar a hukumance

Wata sanarwa da ma’aikatar noma da raya karkara ta ce an kai rahoton dabbobin da ke nuna alamun yiwuwar kamuwa da cutar anthrax a wata gona da ke Suleja a Jihar Neja zuwa ofishin babban jami’in kula da dabbobi na Najeriya a ranar 14 ga watan Yuli.

Ma’aikatar ta ce lamarin ya faru ne a wata gonar dabbobi da ta ƙunshi shanu da tumaki da awaki da ke Gajiri a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna a ƙaramar hukumar Suleja a jihar Neja, inda wasu daga cikin dabbobin ke da alamomi da suka haɗa da zubar jini daga sassan jikinsu, hanci, idanu da kunnuwa.

Ta ce tawagar masu bayar da agajin gaggawa da ta haɗa da ƙwararrun ma’aikatan lafiya na tarayya da na jihar sun ziyarci gonar don gudanar da bincike na farko tare da tattara samfurori daga dabbobin da suka kamu da cutar.

Ma’aikatar ta ce gwaje-gwaje na Cibiyar Nazarin Dabbobi ta ƙasa ta tabbatar da kamuwa da cutar, “wanda ke nuna alamar cutar anthrax ta farko a Najeriya a cikin ‘yan shekarun nan”.

Ta yi nuni da cewa, gwamnatin tarayya ta yi gargaɗi ga ‘yan Najeriya makonnin da suka gabata bayan samun labarin ɓarkewar cutar anthrax a Arewacin Ghana inda duk dabbobin da suka kamu da cutar suka mutu. Sanarwar ta ƙara da cewa gwamnati ta yi kira ga ƴan Najeriya da su gaggauta kai rahoton bullar dabbobin da ke zubar da jini a jikinsu ga hukumomin kiwon lafiyar dabbobi ko kuma ma’aikatan aikin gona.

Comments (0)
Add Comment