Gwamnatin Tarayya ta jaddada cewa babu wanda ya wanda yafi karfin doka, ciki har da shugaban NLC, Comr Joe Ajaero, bayan zarginsa da kin amsa gayyatar hukumomin tsaro.
An kama Ajaero ne a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, yayin da yake shirin tafiya taron Ƙungiyar Ƙwadago ta Biritaniya, TUC a Birnin Landan.
Mai magana da yawun Shugaban Kasa, Bayo Onanuga, ya ce Ajaero ya ki amsa gayyatar hukumar DSS da ke binciken sa.
Ya bayyana cewa, a ƙarƙashin Kundin Tsarin Mulkin kasa, babu wanda ke da ikon bijirewa gayyatar hukumomin tsaro ko bincike na doka.
Ajaero dai ya bayyana cewa an ba shi fasfonsa da wayoyin sa da DSS ta karɓe, bayan kamun da aka yi masa.
Sai dai shi kuma tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya soki kama Ajaero da kuma mamaye ofishin SERAP.
A yanzu dai an samu labarin cewa DSS ta janye jami’anta daga ofishin SERAP da suka yi wa kwanton bauna a baya.